Close Menu
    Facebook X (Twitter) Instagram
    Facebook X (Twitter) Instagram
    ANZO WAJEN
    Advertise With Us
    Friday, December 19
    • Shafin Farko
    • Labarai
    • Yanayi
    • Noma

      Kanfanin Dangote Ya Hada Gwiwa Da Abokan Huddarsa Don Bunkasa Noma

      November 25, 2025
    • Ma’adinai
    • Shari’a
    • Siyasa
    • Tattalin Arziki

      FIDAC Ta Bukaci Kungiyoyin Fararen Hula Su wayar da kan Jamaa akan Sauye-Sauyen Haraji na shekarar 2025 a Najeriya

      December 17, 2025
    • Karin Wasu
      1. Addini
      2. Aikata Laifuka
      3. Al’adu
      4. Harkokin Lafiya
      5. Harkokin Tsaro
      6. Harkokin Waje
      7. Ilimi
      8. Jirwaye
      9. Kimiyya Da Fasaha
      10. Kowane Labari
      11. Kwadago
      12. Nishani
      13. Ra’ayi
      14. Rubutun Zube
      15. Sufuri
      16. Yawon Bude Idanu
      17. Wasanni
      18. View All

      Karin Maganarmu Na Yau

      November 15, 2025

      Kwararren Likita Ya Shawarci “Yan Jarida Kan Lafiyar Kwakwalwa

      November 16, 2025

      An Kammala Taron Sanin Makamar Aiki Na Wakilan Kafafan Yada Labarai Na Jihar Kano A Kaduna

      November 16, 2025

      Kanfanin Dangote Ya Hada Gwiwa Da Kamfanin Honeywell Don Fadada Matatar Mai

      November 26, 2025

      Muna Gabatar Da Sabuwar Jaridarmu Ta Hausa Mai Suna: An zo wajen

      November 14, 2025

      Kuncin Rayuwa, Ya Hana Samari Aure

      November 15, 2025

      Aikin Wucin Gadi: Babban Barazana Ga Ci Gaban Dan Adam

      November 15, 2025
    ANZO WAJEN
    Home » Yanzu A Nigeria,Ruwan Sha Ya Fi Man Fetur Wuyar Samu
    Featured

    Yanzu A Nigeria,Ruwan Sha Ya Fi Man Fetur Wuyar Samu

    Abdullahi YusufBy Abdullahi YusufNovember 17, 2025No Comments3 Views
    images (62)

    Yanzu A Nigeria,Ruwan Sha Ya Fi Man Fetur Wuyar Samu

    Daga Abdullahi Yusuf

    Allah Mai yi da a yi,wai yanzu a kasata ta gado, Nigeria,an wayi gari man fetur ya wadata,har ma ya yi yawa,kamar ya biyo masu ababan hawa har gidajensu.

    Wai a yau,man fetur din da a da a ke nema kamar Ruwan Bagaja, sai ga shi yanzu a na neman kai da shi,masu gidajen mai su na kira,wani zubinma har da rokon masu ababan hawa,domin su zo su saya.

    Idan kuma an saya din,sai ka ga masu sayarda fetur din su na ta fara’a da godiya,kamar ba su ne ba a da su ka rika yin yanga su na gallazawa masu motoci da babura wajen sayar musu da man fetur din.

    An dai sani cewa man fetur din ya wadata ne bayan da Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu ta janye tallafin man fetur, wanda daga nan ne a ka shiga ruguntsumin hada-hadarsa, lokacin da kuma masu gidajen man fetur din su ka boye man fetur din da ke cikin tankunansu,wanda su ka saya da tallafin Gwamnati a ciki.

    Daga nan sai wadannan Bayin Allah su ka rika fito da tsohon man fetur din da su ka saya a kan farashin N230 ko sama da haka, a kan lita daya, a lokacin tallafi, da kadan-kadan,su na sayar da shi N900 a kan lita daya,har sai da man ya kai N1,500 lita daya,kuma ma babu shi a gidajen man.

    Wannan halin ya sanya tilas masu ababan hawa da yawa su ka hakura da man fetur din.Wadansu daga cikinsu ma suka sayarda motocinsu,wadansu su kuma su ka koma amfani da babura domin samin sauki.

    Da sannu,sai farashin man ya rika saukowa, har ya kai a na sai da shi kasa da N1000 a yanzu,sai dai matsalar ita ce yawancin mutane ba sa iya sayensa da yawa saboda halin matsin tattalin arzikin da a ke ciki.

    Sai ka ga mutum ya zo gidan mai da babbar mota ya ce a zuba masa na N5000,abin takaici, abin tausayi.Wannan halin ne ya sanya man fetur din ya taru tinjim a gidajen man,a na so a saya,amma ba bu kudin sayen.

    Saboda haka yanzu a Nigeria, man fetur ya fi saukin samu a saya,fiye da ruwan sha, musamman ma a wasu garuruwan da masu karamin karfi ke zaune.

    Za ka ga mai sayar da ruwa a cikin kura a na kiransa ya na yanga, ya na wulakanta masu saya,har ya na fada musu bakaken maganganu,amma a waje daya masu sayarda man fetur su na roko a zo a saya.

    Wannan yanayi ba wani ci gaba ba ne,kawai nuni ne ga yadda kasuwar man fetur ta kasance a halinzu, wato,”Ga Koshi Ga Kwanan Yunwa.” Allah Shi kyauta.

     

    Share. Facebook Twitter WhatsApp Telegram
    Abdullahi Yusuf

      Related Posts

      KARIN MAGANARMU NA YAU:

      December 17, 2025

      KARIN MAGANARMU NA YAU:

      December 16, 2025

      Gidauniyar Bashir Da UNFPA Sun Koyawa Mata 25 Sana,oi A Gusau

      December 15, 2025
      Leave A Reply Cancel Reply

      Top Posts

      Daruruwan Mutane Sun Halarci Jana’izar Ado Lamco, a fadar masarautar Kano

      November 22, 202517

      Kimanin Mata Miliyan 68  Sun Fuskanci Shayi A Najeriya .

      December 10, 202511

      Muna Gabatar Da Sabuwar Jaridarmu Ta Hausa Mai Suna: An zo wajen

      November 14, 202511

      KARIN MAGANARMU NA YAU

      December 8, 20258
      Connect With Us
      • Facebook
      • Twitter
      • Instagram
      • YouTube
      • LinkedIn
      • TikTok
      • Telegram
      • WhatsApp
      Don't Miss
      Tattalin Arziki

      FIDAC Ta Bukaci Kungiyoyin Fararen Hula Su wayar da kan Jamaa akan Sauye-Sauyen Haraji na shekarar 2025 a Najeriya

      By Abbas IbrahimDecember 17, 2025

      Kungiyar tabbatar da da,a da daidaito akan al’amuran kudade da cigaban Al umma wato…

      KARIN MAGANARMU NA YAU:

      December 17, 2025

      KARIN MAGANARMU NA YAU:

      December 16, 2025

      Gidauniyar Bashir Da UNFPA Sun Koyawa Mata 25 Sana,oi A Gusau

      December 15, 2025
      © 2025 ANZO WAJEN. Developed by: ENGRMKS & CO.
      • Home
      • About Us
      • Advertise With Us
      • Contact Us
      • Disclaimer
      • Privacy Policy

      Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.