
An kammala taron kwana huɗu da asusu majalisar dinkin duniya (UNFPA) ta shirya a hotel din Tahir dake garin kano, kan inganta kyawawan halayen maza, inda mahalarta suka ƙirƙiro tsare-tsare na ayyuka domin magance aurar da ƙananan yara, kaciya ga mata (FGM), da kuma cin zarafin jima’i da na jinsi (SGBV).

Mahalarta taron, waɗanda suka fito daga kungiyoyin matasa da na al’umma daban-daban, ana sa ran za su fara aiwatar da ayyukan da aka tsara kafin 31 ga watan Disambar shekarar ta 2025.

Da take jawabi a Yayin rufe taron, jami’ar UNFPA Hajiya Bahijja Bello Garko ta tabbatar da kudirin hukumar na ci gaba da yaƙi da matsalolin zamantakewa ta hanyar inganta kyawawan halayen maza.

Ta ce an zaɓi mahalarta taron a matsayin manyan masu horaswa ne bisa cancanta da kuma aikin su na baya, inda ta nuna cikakkiyar gamsuwa da yadda za su iya aiwatar da abin da suka koya.

Hajiya Bahijja ta yaba da jajircewar da mahalartan suka nuna tsawon lokacin taron, tana mai cewa an shirya taron ne domin ƙara musu ƙwarewa wajen jagorantar wayar-da-kai a cikin al’ummominsu.
Ta kuma tunatar da su muhimmancin kula da al’ada da dabi’un al’umma yayin yin aikin wayar-da-kai domin gujewa kin karbar abinda suka zo dashi
A nata jawabin, Hajiya Karima Bungudu ta yi Karin gaske, a kan illolin munanan halayen maza ga cigaban al’umma, tana mai jaddada bukatar mayar da hankali wajen canza tunani da dabi’un da ke haifar da wariya da tashin hankali.
Ta shawarci mahalarta taron, da su ci gaba da mayar da hankali yayin yada horon a garuruwansu.
Masu gabatar da darussa, Dr. Olusegun Medupin da Dr. Auwalu Hallilu, sun jagoranci zaman rubuta rahoto, da Samar da hanyar kuɗaɗen gudanar da aiki, da illolin halayen maza marasa kyau ga jama’a.
Da yawa daga cikin mahalartan sun bayyana taron a matsayin mai tasiri kuma mai sauya tunani, inda suka gode wa malamai bisa zurfin ilimi, da yadda suka gudanar da darussa cikin fasaha, da kuma jajircewarsu wajen gina sabuwar al’umma masu rajin daidaito tsakanin jinsi.

