Daga Mustapha Muhammad
Yawaitar Al’ummar Jihar Kano dake Arewa maso Yammacin Najeriya cikin hanzari, ta kasance wani babban abin damuwa, musamman a ƙoƙarin samar da isasshen abinci da aikin yi da tallafawa matasa da mata. Hakan ce ta sa karfafa wa manoma gwiwa domin noma ƙarin hatsi da nau’in tsirrai masu yaɗo, har ma da fito da hanyoyin daga darajar amfanin gona yake da matukar muhimmanci.
Saboda haka ne Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tsaya kai da fata wajen sauya fasalin harkar noma a fannoni uku: haɓaka samar da amfanin gona, sarrafawa da kuma kasuwanci.
A cikin tsarin gangamin yakin neman zabensa na shekarar 2023, ya yi alƙawarin kawo sauyi a bangaren noma ta hanyar inganta noman zamani, wayar da kan manoma su rungumi ingantaccen tsarin noma na zamani da samar da managarcin iri, tare da ba da tallafin kayan aikin gona.
Bari mu fara duba irin ƙoƙarin da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi wajen inganta harkar noma a Kano, ta hanyar ambata wasu nasarorin wani muhimmin shiri daga cikin gwamman ire-irensa da ake aiwatarwa a Kano. Wannan kuwa shi ne Shirin Bunkasa Noma da Kiwo na Jihar Kano wato KSADP a takaice.
Shirin KSADP wanda Bankin Musulunci (IsDB), da kungiyar Live and Livelihood Fund (LLF) tare da Gwamnatin Kano ke ɗaukar nauyi, ya ba da muhimman tallafi don ƙara samar da abinci, rage talauci da inganta rayuwar jama’ar Jihar Kano.
Jihar Kano, wadda tafi kowace jiha yawan jama’a a ƙasar nan, na da yalwar ƙasar noma na damina da rani wanda ya dace da zamani. Shirin KSADP ya mayar da hankali kan bunkasa noman hatsi da kayan gona dangin legumes tare da fito da darajar amfanin gona. Sama da mutane miliyan 1.2 ne suka amfana kai tsaye, yayin da ɗaruruwan dubban mutane suka amfana a ba ta kai tsaye ba.
Hukumar Bunkasa Aikin Noma ta Kano wato KNARDA, kasancewarta daya daga cikin hukumomin aiwatarwa, na da alhakin babbaka nau’in amfanin gonar masu yaɗo da ake kira legumes, yayin da SASAKAWA ke kula da bangaren hatsi wadanda kuma dukansu sun samu gagarumar nasara.
Tallafin da aka mayar kan amfanin gona nau’in legumes kadai, da suka hadar waken soya, waken Hausa da kuma gyada, ya kai ga manoma dubu dari, ciki har da matasa da maza da kuma mata, a matakai uku na nomawa da sarrafawa da kuma kasuwanci. Waɗannan nau’ukan kayan gona na da matukar amfani ga mutane da dabbobi, kuma ana iya noma su sosai a dukkan sassan jihar Kano.
Shirin ya koyar da manoma dabarun noma na zamani domin su ƙara yawan amfanin gona tare da ribar da suke samu.
Jami’an fasahar noma na hukumar ta KNARDA sun nuna yadda ake amfani da karamin fili wajen noma abinci mai yawa, da nufin nuna bambanci tsakanin tsohon tsarin noma da kuma ingantaccen tsarin zamani.
Bugu da ƙari, an gabatar da sabbin iri na waken soya da waken Hausa da gyada, tare da taimaka musu wajen nomawa da kuma yaɗa su.
Cibiyoyin bincike na IITA da ICRISAT sun samar da ingantattun iri masu jurewa fari, da kuma samar da abinci ga dabbobi.
Matakin ya yi nasara matuka, domin manoma sun gwada sun gamsu, suna ci gaba da yaɗa irin a kananan hukumomi 44 na jihar nan.
Yawan amfanin gona da abincin dabbobi da ake samu a karshen kaka, ya ƙara wa manoma kwarin gwiwa l, har wasu daga ciki suka zama masu harkar samar da iri.
Shirin ya gano muhimman hanyoyin kara darajar amfanin kayan gonar bayan girbi, ciki har da ƙara lafiyar abincin mu da tabbatar da wadatarsa. Hakan ya samo asali ne daga kayan abinci da ake sarrafawa irin su garin bul-bul dake zama nau’in abinci mai gina jiki da dai sauransu.
Hukumar KNARDA tare da KSADP sun horar da kungiyoyin mata kan yadda za su sarrafa wadannan kayan abinci mai gina jiki daga kayan gonar.
Hakan ya taimaka wajen ciyar da yara abinci mai inganci tare da samar wa matan hanyar samun kuɗin shiga.
Ƙarin wasu ƙungiyoyin matan kuma an tallafa musu da injunan matsar mai, domin rage talauci da kuma shiga harkokin kuɗi ka’in da na’in.
Matan da aka horar sun taimaka wa iyalansu, kuma sun fara haɗa kai don kafa ƙananan masana’antu domin faɗaɗa harkokinsu.
Baya ga samar da injunan matsar mai ga wadannan mata, shirin zai kuma tallafawa kungiyoyin mata 100, kowacce kungiya na da mata 25, jimilla mata 2,500.
Shirin ya sauya rayuwar dubban mata, musamman a yankunan karkara.
Bincike ya gano cewa waken, wanda daya ne daga cikin nau’ikan amfanin gonar da ake magana a kai, yana buƙatar feshin magani akai-akai don samun ingantacciyar yabanya. Saboda haka ne, shirin ya horar da matasa 700 kan hanyoyin feshin mafi inganci.
Sun koyi yadda ake feshin da lokacin da ya dace a yi feshin da kuma kayan ba da kariya.
A da feshin yana iya yi wa mai feshi illa, amma yanzu an basu horo kan tsarin feshin da ake amfani da shi a duniya tare da kayan samun kariya.
Ɗaya daga cikin manyan kalubalen manoma shi ne rashin samun kuɗi. Wannan ta sa gwamnatin Abba Kabir Yusuf, karkashin hukumar KNARDA da shirin KSADP, ta shirya tattaunawa tsakanin manoma da cibiyoyin ba da lamunin kuɗi domin sanar da su yadda ake samun rance.
Babu shakka, shirin KSADP kan noman gyada da waken soya da kuma waken Hausa ya samu babbar nasara ta hanyar sauya rayuwar dubban manoma kai tsaye da ma wadanda ba kai tsaye ba.
Baya ga haka, ƙoƙarin hukumar KNARDA wajen haɗa manoma da kasuwanni, musamman kasuwar hatsi ta Afrika ta Dawanau, ya buɗe sabuwar kafa gare su ta sayar da gonarsu.
A takaitacce, shirin ya samar da ingantattun iri, ya koyar da dabarun noma na zamani, ya samar wa matasa ayyukan yi, ya ƙarfafa wa mata wajen samar da sinadaran abinci mai gina jiki da yaki da cutar tamowa.
A wata hira da aka yi da shi l, Manajan Daraktan hukumar KNARDA, Dr. Farouk Ahmad Kurawa, ya ce:
> “Ina hango Kano ta koma matsayin jagora a fannin noma kamar yadda ta ke a zamanin mulkin Audu Bako.”
Shi ma Shugaban Shirin KSADP, Alhaji Ibrahim Gama, ya shaida wa manema labarai cewa:
> “Abu mafi farin ciki a gare ni shi ne ganin manoma sun rungumi sabbin dabarun noma na zamani.”
Wannan gagarumin sauyi a fannin noma ba komai ba ne face somin tabi, akwai sauran bayanai da za su zo a rubuce-rubuce na gaba.
Babu ko shakka, sauya fasalin harkokin noma shi ne babban abin alfahari na Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Mustapha Muhammad, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Kano, daga Birnin Kano.
