Sarkin Kano Sunusi Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Ga Wadanda Harin “Yan Bindiga Ya Shafa A Garin Shanono
By Abdullahi Yusuf
Sarkin Kano,Khalipha Muhammadu Sanusi II,ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalai da kuma wadanda harin “Yan Bindiga ya rutsa da su a garin Faruruwa da ke cikin Karamar Hukumar Shanono, a kwanan baya.
Wata sanarwa da Shugaban Ayarin “Yan Jarida masu dauko labarai daga Fadar Kano,Sadam Na’ando Yakasai,ya bayar,ta ce Sarkin ya yi ta’aziyya ga mutanen da harin ya shafa a garin na Faruruwa.
Sanarwar tace yayin ziyarar, Sarkin ya yi addu’a ga Allah da ya jikan wadanda su ka rasu a sakamakon harin, ya kuma bai wa iyalan mamatan hakurin wannan rashi.
Sarkin,ya kuma yi kira ga mazauna yankin na Shanono da su zama masu kaffa-kaffa tare da lura da yanayin tsaro a wannan shiyya,su kuma kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro domin a yi maganinsa nan take.
Daga nan sai Sarkin ya yi kira ga mazauna yankin na Shanono da kuma mutanen Jihar Kano ba ki daya, da su yi ta addu’a domin samun zaman lafiya,kwanciyar hankali da hadin kai a Jihar Kano da Nigeria ba ki daya.
A cikin jawabinsa yayin ziyarar,Hakimin Shanono kuma Dankadan Kano, Dr. Bashir Ibrahim Muhammad, ya gode wa Sarkin saboda wannan ziyara da ya kai,wadda ya ce nuni ce ga irin yadda ya damu da rayuwa da walwalar talakawansa.
Dr.Bashir ya yi addu’a ga Allah da ya taimaki Sarki,ya kuma kara yi masa jagora wajen kokarin da ya ke yi na tafiyar da mulkin Kano.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar ta Shanono,Ahaji Barau Abubakar,ya jaddada kudirin Karamar Hukumar na ci gaba da daukar duk wasu matakai da su ka dace domin yin maganin matsalar tsaron da ta addabi yankin.
Daga nan sai Shugaban Karamar Hukumar ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano saboda irin kokarin da ta ke yi domin kawar da matsalar hare-haren “Yan Bindiga daga yankin.
