
Shahararren Wanzami, Alhaji Musa Kawu Wanzami, ya bayyana rasuwar ɗan kasuwar Kano, Alhaji Ado Aminu (Mai Shinkafa), wanda aka fi sani da Alhaji Ado Lamco, a matsayin babban rashi da ya bar gibi mai wahalar cikewa.
Alhaji Musa Wanzami, wanda ke gudanar da harkokinsa kusa da Lamco Pharmacy da ke kusa da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), ya ce ya shafe fiye da shekaru 20 yana tare da marigayin. Ya bayyana Alhaji Ado a matsayin mutum mai karamci, sauƙin kai da tausayi, wanda ya taɓa rayuwar mutane da dama ta hanyar ayyukan alheri.
A cewarsa, Alhaji Ado Lamco ya rayu rayuwa abin koyi, kullum a shirye yake ya tallafa wa marasa ƙarfin hali da kuma inganta walwalar mutanen da ke kewaye da shi.

Wani maƙwabcin marigayin shima na tsawon shekaru 20 , Malam Inusa Mai Lemo, wanda ya zauna a yankin tun lokacin da aka kafa kantin maganin, ya kuma tuna yadda marigayin yake tsayawa tsayin daka wajen tallafa wa masu buƙata. Malam Inusa, da ke sana’arsa a gaban masallacin da Alhaji Ado ya gina, ya ce Jama,a na amfani da masallacin, inda suke tabbatar da kirkin mamacin.

Dukkaninsu sun yi addu’a ga Allah Ya jikansa, Ya yi mashi gafara ya kuma baiwa iyalansa juriya wannan babban rashi.
Alhaji Ado Lamco, mai shekaru 70, ya rasu ne a ranar Litinin, 17 ga Nuwamba, a wani asibiti da ke birnin Cairo, a masar, inda yake karɓar magani. Marigayin ɗan kasuwa , a fannin kiwon lafiya, ya bar ’ya’ya 15 — maza 10 da mata 5.
An gudanar da sallar jana’izarsa ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, inda daruruwan mutane suka halarta suka kuma raka gawarsa zuwa makabartar Dandolo, inda aka yi mashi sutura cikin hawaye da alhini daga iyalai, abokai, ’yan kasuwa da al’ummar yankin.
