Muna Gabatar Da Sabuwar Jaridarmu Ta Hausa Mai Suna: An zo wajen
A duk rayuwar Dan Adam,a kan sami al’amura ko na Zamantakewa,ko na Tattalin Arziki,ko na Siyasa,wadanda su ka sha kan mutane,wadanda kuma a ke ta Muhawara a kansu domin a sami masalaha ko matsaya.
Da zarar an sami daidaito a kan wani Mauru’i sai ka ji a na cewa,”An zo wajen.” Haka kuma duk lokacin da Jama’a su ke jiran wata sanarwa a kan wani abu muhimmi,ko wani Albishir,to, da zarar an sanar da shi,sai ka ji an ce, “An zo wajen.”
Jama’ar Arewa sun dade su na jiran wata Jarida ko Mujalla wadda za ta rika kawo musu fitattun labarai a kan wasu mahimman al’amura a cikin tsagwaron harshen Hausa.Kwatsam,sai ga wasu Bayin Allah sun bijiro da wata Jarida wadda su ka lakabawa suna, “Anzowajen.”
Saboda haka,muna farin cikin gabatar muku da Jaridar Hausa,Anzowajen,mallakar Kanfanin StraightWaves Media Services, wadda za a rika bugawa ta hanyar Yanar Gizo,wato anzowajen.com.
Ita wannan Jaridar ta musamman,za ta rika kwararo muku labarai da su ka shafi dukkan fannonin rayuwar Dan Adam,kama daga Zamantakewa, Tattalin Arziki,Siyasa,Wasanni,harkokin Tsaro,Shari’a da sauransu.
A wajen rubutawa da buga labaranmu za mu kasance masu tsage gaskiya komai dacinta,ba sani ba sabo,tare da bai wa kowa hakkinsa.
Ku biyo mu ku sha ingantattun labarai.An zo wajen.Mun gode.
Naku,
Abdullahi Yusuf
Babban Edita
