Kwararren Likita Ya Shawarci “Yan Jarida Kan Lafiyar Kwakwalwa
Daga Abdullahi Yusuf
Wani kwararren Likitan kula da Lafiyar Kwakwalwa,Dr. Aminu Ibrahim Shehu, ya shawarci “Yan Jarida da su rika lura da lafiyar kwakwalwarsu sosai, domin cigaban aikinsu.
Dr.Aminu Ibrahim Shehu,wanda ke aiki a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke Kano,wato AKTH,ya ce hakan ya zamo dole,in an yi la’akari da yawan samun korafe-korafen galabaita da damuwar kwakwalwa a tsakanin “Yan Jarida.
Ya ba da wannan shawarar ne a yayin da ya ke gabatar da wata Makala a kan galabaita da damuwar da “Yan Jarida ke fuskanta yayin gudanar da aikinsu,a wani taron Sanin Makamar Aiki da Kungiyar Wakilan Kafafan Yada Labarai Na Jihar Kano,wato(Correspondents’ Chapel),ta shirya domin “Ya “Yanta,wanda ke gudana a garin Kaduna,a halin yanzu.
Ya ce, “Yan Jarida,kullum su na cikin gaggawar hada labaru don su buga su domin amfanin Jama’a,wanda shi ke sanyawa su ke galabaita da samun damuwa a kwakwalwarsu.
Kwararren Likitan ya ce,ya kuma lura cewa,”Yan Jarida,kamar masu aikin Soja su ke,inda su kan ga abubuwan ban tsoro yayin da su ke gudanar da aikinsu.
Ya ce, wannan al’amarin ma ya kan sanya su samu damuwa kwarai da gaske,wanda kuma ya ka iya tauye aikinsu.
Saboda haka,tilas ne,in ji Dr.Shehu, “Yan Jarida su rika kula da lafiyar kwakwalwarsu sosai, in ba haka ba, a na iya samun raguwar masu Aikin Jarida saboda matsalolin da su ka shafi ciwon damuwa, har ma da kashe kai.
Daga karshe, kwararren Likitan ya shawarci “Yan Jaridar da su rika kula da lafiyar jikinsu,ciki har da yin barci isasshe,su kuma rika neman taimakon kwararrun Likitoci yayin da duk su ka shiga cikin mummunar galabaita da damuwa.
