Kanfanin Dangote Ya Hada Gwiwa Da Kamfanin Honeywell Don Fadada Matatar Mai
Daga Abdullahi Yusuf
Kamfanin Dangote ya hada gwiwa da Kamfanin Honeywell International Inc don tallafawa wajen aiwatar da kashi na gaba na fadada Matatar Mai ta Dangote.
A karkashin wannan hadin kan, za a samar da wata babbar fasaha da za ta sanya Matatar Man ta rika tace danyen man fetur ganga miliyan 1.4 a rana,wanda zai sanya a cinma burin Matatar Man ta zamo mafi girma a duniya a shekarar 2028.
Sannan kuma Kamfanin na Honeywell zai samar da wasu na’urori na musamman wadanda za su sanya Matatar Man ta rika tace danyen mai iri dabam-dabam
Shi dai kanfanin Honeywell kwararren ne wajen samar da dabarun sarrafa harkokin masana’antu dabam-dabam a duk fadin duniya.
Tun cikin shekarar 2017 ne Kamfanin na Honeywell ya ke hudda da Kamfanin Dangote wajen samar da dabarun tace danyen man fetur da sauransu.
Shi kuma Kamfanin na Dangote tuni ya fara amfani da dabarun da ya samu wurin Honeywell wajen iya samar da sinadarin Polypropylene har tan miliyan 2.4 a shekara.
Haka kuma Kamfanin na Dangote na samun ci gaba wajen bunkasa samar da takin zamani,inda zai kara yawan taki samfurin urea da ya ke sarrafa wa daga miliyan uku zuwa miliyan tara a shekara.
