Kanfanin Dangote Ya Hada Gwiwa Da Abokan Huddarsa Don Bunkasa Noma
Daga Abdullahi Yusuf
Shahararren kanfanin nan na Dangote Group ya hada gwiwa da abokan huddarsa domin bunkasa harkokin noma a Nigeria.
Wata sanarwa wadda mai magana da yawun kanfanin,Anthony Chiejina, ya sanya wa hannu, tace wannan yunkuri ya zo ne daidai lokacin da kanfanin ya dauki nauyin Bikin Nuna Fasahar Noma Na Kasa, karo na sha bakwai, wanda a ke farawa a birnin Keffi da ke cikin Jihar Nasarawa, a yau Talata,25 ga watan Nuwamba.
Chiejina ya ce bunkasa aikin noma ta hanyar amfani da na’urorin zamani zai bunkasa arzikin kasa,ya kuma samar da aikin yi ga matasan Nigeria.
Ta hanyar wannan hadin gwiwa,in ji shi, kanfanin na Dangote ya ke kokarin bunkasa noman amfanin gona na sayarwa,domin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Ya ce taken wannan bikin na nuna fasahar noma na kasa shine,”Karfafawa Kananan Manoma Gwiwa Don Bunkasa Noma,” zai taimaka wajen samar da abinci ga “Yan Kasa.
Ya ce idan har aka bunkasa noma,to za a bunkasa tattalin arkin kasa,samar da isasshen abinci da kuma aikin yi ga “Yan Kasa.
Mai magana da yawun kanfanin Dangoten, ya kara da cewa bikin na nuna fasahar noma zai kuma daidaita lokutan aikin noma,da kuma samar da sabbin dabarun noma.
Ya ce a halin yanzu, kanfanin na Dangote,ya na samar da masana’antun casa shinkafa a jihohin Kano, Jigawa, Niger, Kebbi, and Sokoto, wadanda za su iya casa shinkafa tan miliyan 1.5 a shekara.
Ya ce wannan ya na daga cikin kokarin kanfanin na taimakawa Gwamnati wajen samar da isasshen abinci ga kasa.
Daga nan sai sanarwar ta ambato babbar mai bai wa Shugaban gungun kamfanonin Dangote shawara,Fatima Wali-Abdurrahman, ta na cewa a cikin yunkurin kanfanin na sarrafa kayan gona a Nigeria, ya na zuba jari a bangaren samar da sukari a jihohin Nasarawa da Adamawa.
Fatima ta kuma ce a yanzu haka, kanfanin na Dangote ya kafa kanfanin samar da takin zamani mai fitar da tan miliyan uku na taki,a Lekki Free Trade Zone da ke Jihar Lagos.
Shugaban kwamitin amintattu na Kungiyar Bunkasa Noma ta kasa, wadda ita ce ta shirya bikin,Arc Kabiru Adamu, ya ce kanfanin Dangote babban abokin huddarsu ne da dadewa,wanda ya ke taimaka musu kwarai wajen shirya bikin.
Arc Kabiru Adamu, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Manoma ta kasa,wato AFAN,ya yi kira ga kanfanin na Dangote da ya mayar da hankali wajen bunkasa noma,bayan da ya ci nasara a kasuwar mai da gas.
Ya ce a na sa ran cewa bikin zai samu halartar manyan manoma, masana’antu,masu bincike,matasa da mata manoma,duka a cikin taimakonsu na bunkasa samar da abinci a cikin kasa.
