Gwamna Abba Yusuf Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na N1.3trn Ga Majalisar Dokokin Jihar Kano
Daga Abdullahi Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudi na N1.368 trillion na shekarar kudi ta 2026 ga Majalisar Dokokin Jihar Kano,a ranar Laraban nan.
Kasafin kudin Mai taken,” Kasafin Kudi Na Gudanar Da Mahimman Ayyuka Da Cigaban Kasa Mai Dorewa,” wani shiri ne na kashe kudi domin gudanar da ayyukan raya kasa a duk fadin jhar,in ji Gwamnan.
Ya ce Kasafin Kudin,an tsarashi ne domin kammala wasu manyan ayyukan da aka fara a duk fadin Jihar,tare da bullo da wasu sabbin tsare-tsare don bunkasa tattalin arzikin Jihar.
Gwamnan ya ce an ware kaso mai tsoka daga cikin Kasafin Kudin domin gudanar da mahimman ayyuka kamar yadda a ka zayyana a cikin kudirin Gwamnatinsa na gudanar da manyan ayyuka da bunkasa ci gaban Jihar.
Ya ce daga cikin kudin,an ware N934.640 billion domin gabatar da manyan ayyuka, yayin da za a kashe N433.487 billion domin ayyukan yau da kullum.
Gwamnan ya kara da cewa, Kasafin Kudin ya na dauke da burin gudanar da ayyukan da za su bunkasa rayuwar mutanen Jihar,ciki har da gina hanyoyi,samar da ruwan sha,tsaro,tallafi da bunkasa birane.
Saboda haka, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci Majalisar Dokokin da ta duba da kuma amince da Kasafin Kudin a kan lokaci, domin a samu damar gudanar da ayyukan da ta kunsa a cikin shekarar kudi ta badi.
Da ya ke mayar da jawabi, Shugaban Majalisar, Alhaji Jibril Fagore, ya gode wa Gwamnan saboda mulkin gaskiya da adalci
da ya ke gudanarwa a Jihar,ya na mai ba shi tabbacin Majalisar na duba Kasafin Kudin cikin tsanaki kuma a kan lokaci.
Falgore,ya kuma yabawa bangaren zartaswa na Jihar saboda akin da ta ke yi kafada-da-kafada da Majalisar domin ci gaban Jihar.
