Kungiyar tabbatar da da,a da daidaito akan al’amuran kudade da cigaban Al umma wato Fiscal Discipline and Development Advocacy (FIDAC) ta yi kira ga kungiyoyin fararen hula (CSOs) da su bayar da muhimmiyar gidunmowa wajen tabbatar da aiwatar da Dokokin Sauye-sauyen Haraji na shekarar 2025 tana mai jaddada cewa nasara ba kawai a wayar da kai take ba akwai bukatar shigo da Al umma
A cikin wata sanarwa da shugaban ta, Abdussalam Muhammad Kani, ya fitar ya bayyana sauye-sauyen harajin a matsayin wani mataki na zamanantarwa tare da inganta tsarin haraji na Najeriya,da kuma fadada hanyoyin samar da kudin shiga da kare masu karamin karfi, da kuma karfafa dangantaka tsakanin biyan harajin da ci gaban kasa.
FIDAC ta ce tasirin wadannan sauye-sauyen zai dogara ne da fahimtar jama’a tare da amincewar su, da kuma bin doka da oda
Kungiyar ta gargadi cewa tsarin sabbin dokokin na da rikitarwa wanda zai yi wahalar fahimta wajen jama’a idan ba a fassara musu su yadda ya dace ba.
Kungiyar ta bukaci kungiyoyin fararen hula da su fassara sauye-sauyen yadda Al umma zasu fahimta ta hanyar wayar da kan al umma da shirye-shiryenabijin da kuma amfani da kafafen sada zumunta tare da hada kai da ‘yan kasuwa kanana da matsakaita da sauransu
Daga cikin muhimman sauye-sauyen, FIDAC ta jaddada cewa wadanda ke samun kudin da basu haura naira ₦800,000 a shekara ba,ba za su biya haraji ba, yayin da kuma kananan ‘yan kasuwa za su amfana da tallafin kudin haya har zuwa ₦500,000.
Yayin da Najeriya ke komawa tsarin haraji na zamani wato digital da suka hadar da e-invoicing da electronic filling
FIDAC ta bukaci kungiyoyin fararen hula da su isar da sakon ta yanar gizo da kuma bayyana alfanunsa domin karfafawa Al umma.
Ta kuma bukaci a samar da tallafi da saukakawa wajen yin rajistar TIN da sauran tsarukan haraji.
FIDAC ta jaddada bukatar yin gaskiya da rikon amana, inda ta bukaci kungiyoyin fararen hula da su bukaci bayanai daga gwamnati kan yadda ake amfani da kudaden haraji da kuma sa ido kan yadda ake aiwatar da dokoki domin kare masu karamin karfi.
FIDAC ta ce dokokin sauye-sauyen haraji na 2025 wata babbar dama ce ga kungiyoyin fararen hula wajen karfafa gwiwa da amincewa da tsarin haraji, domin hakan wani ginshiki ne da zai taimaka wajen ci gaban kasa.
