
Mata ashirin da biyar (25) da suka Samu Lafiya daga cutsr yoyon fitsari a Gusau, Jihar Zamfara, sun kammala wani shirin koyon sana’o’i da Gidauniyar Bashir Foundation for Fistula and Women’s Health Rehabilitation ta shirya, domin dawo da mutuncinsu da kuma ƙarfafa su su dogara da kansu.

Jagorar shirin, Nafisa Balarabe Abdullahi, ta bayyana cewa an horas da waɗanda suka ci gajiyar shirin a harkokin yin man shafawa (pomade) da kuma yin kayan ado na beads, sannan aka ba su kayan farawa domin su samu damar fara ƙananan sana’o’i.

Ta ce shirin, wanda Asusun Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yawan Jama’a (UNFPA) ya ɗauki nauyinsa, ya kuma haɗa da darussan wayar da kai kan lafiyar mata, musamman lafiyar haihuwa da jin daɗin rayuwa.

Nafisa Abdullahi ta ƙara da cewa shirin ya mayar da hankali kan matsalolin fistula ta haihuwa (obstetric fistula), tare da jaddada hanyoyin rigakafi, gano matsala da wuri, da kuma muhimmancin zuwa cibiyoyin lafiya lokacin daukar ciki da haihuwa.

Da yake jawabi a wajen taron, likitan fiɗa na VVF da ke aiki da shirin, Dr. Musa Birnin Tasaba, ya ilmantar da waɗanda suka ci gajiyar shirin kan matakan kariya domin kauce wa sake kamuwa da cutar.
Dr. Tasaba ya kuma wayar da kan matan kan lafiyar uwa da tsaftar jiki, yana kawo misalai na abubuwan da ake iya kaucewa da kan haddasa fistula, musamman nakudar haihuwa mai tsawo ba tare da samun kulawar likita a kan lokaci ba.

Haka kuma, ya ba su shawarwari kan damammaki da hanyoyin samun tallafin kuɗi (grants) domin ƙarfafa su wajen samun ’yancin tattalin arziƙi da dogaro da kai na dogon lokaci.
A nasu jawaban, waɗanda suka tsira daga cutar sun nuna godiya sosai ga Gidauniyar Bashir da UNFPA bisa wannan tallafi, inda suka bayyana shirin a matsayin abin da ya sauya rayuwarsu bayan shafe shekaru suna fama da raɗaɗi da ƙyamar al’umma.
Sun kuma yi addu’ar samun nasara da ci gaba ga gidauniyar da abokan hulɗarta, suna cewa tallafin ya ba su sabon fata, mutunci da sabon farawa a rayuwa.
