Rundunar Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta kasa dake Kano (NDLEA) ta sake jaddada aniyarta ta kara kaimi wajen yaki da shan miyagun kwayoyi a fadin jihar.
Kwamandan Rundunar , CN DY Lawal, ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar shugabar kungiyar Kare Al’umma Daga Shan Miyagun kwayoyi (LESPADA), Ambasada Maryam Hassan, a ziyarar ban girma data kaiwa kwamandan.
Ya bayyana manyan nasarorin da hukumar ta samu wajen yakar shan miyagun ƙwayoyi,
ya jaddada cewa yaki da miyagun kwayoyi alhakin kowa da kowa ne, kuma yana bukatar hadin gwiwar dukkan masu ruwa da tsaki.
CN Lawal ya lura cewa NDLEA ba za ta iya yin nasara ita kaɗai ba, don haka ya yi kira ga jama’a da su bayar da sahihan bayanai, tare da tabbatar da cewa duk wani bayani da aka bayar za a kiyaye sirrinsa yadda ya kamata.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa wajen hada kai da LESPADA domin kawar da shan miyagun kwayoyi a cikin al’umma.

Tun da farko, Ambasada Maryam Hassan ta yaba wa rundunar bisa jajircewa da kwazon da take nunawa wajen yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi, inda ta bayyana kokarin NDLEA a matsayin muhimmi wajen kare al’umma, musamman matasa.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Mataimakin Sufiridanda na Miyagun kwayoyi, Sadiq Muhammad Maigatari, ya fitar, an ambato Kwamandan yana jaddada muhimmancin tsarin hadin gwiwar al’umma wajen samun nasara a yakin da ake yi da shan miyagun kwayoyi.
