
Yau Talata ta kasance kwanaki takwas , da rasuwar mamallakin shagunan siyar da maganguna na Lamco Alhaji Ado Aminu Mai Sh inkafa wanda aka fi sani da Alhaji Ado Lamco, Daya daga cikin manajojinsa, Malam Abdullahi Idris ya bayyana dalilin da yasa aka cigaba da siyar da magunguna a shagunan duk da rasuwar mai shagunan.
Da yake Jawabi a masallacin da Alhaji Ado Lamco ya gina, bayan rasuwarsa, Malam Abudullahi Idris yace tun lokacin marigayin yana raye ya bayar da wasiyya cewa ko bayan ya rasu a cigaba da siyarwa al’umma magunguna a shagunan.
Yace marigayin ya jaddada cewa ko bayan ya rasu kada a rufe shagunan saboda wanda suka dogara da shagunan musamman marasa lafiya da yan’uwan su dake asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da wasu shagunan dake sassan jihar nan.
Malam Abdullahi Idris yace bayan rasuwar marigayin iyalan sa sun bada umarnin aiwatar da wasiyyar daya bayar.
Yace Lamco ya shafe shekaru ashirin da kafuwa yana gudanar da cinikayyar magunguna da kayayyakin kula da lafiya a jihar nan da wasu jihohi dake makotaka da Kano har ma da kasashen Cameroon da Chadi da Jamhuriyar Niger.
Ya bayyana Alhaji Ado Lamco a matsayin mutumin kirki mai hakuri Wanda yake mu’amala da mutane bisa girmamawa wanda yayi adduar Allah SWT ya jikan sa ya sashi a aljannar firdausi.
Alhaji Ado Lamco ya rasu a wani asibiti dake kaşar Cairo yana da shekaru da saba’in wanda bayan kawo gawar sa nan gida Kano Mai Martaba şarkın Kano Alhaji Muhammad Sunusi II ya jagoranci yi masa salla daya samu halattar dubban mutane kuma aka binne shi a makabartar Dandolo.
Alhaji Ado Lamco ya bar yaya goma sha biyar da suka hadar da maza goma da mata biyar.
