An Kammala Taron Sanin Makamar Aiki Na Wakilan Kafafan Yada Labarai Na Jihar Kano A Kaduna
Daga Abdullahi Yusuf
A yau,16 ga watan Nuwamba 2025, ne a ka kawo karshen taron Sanin Makamar Aiki na Kungiyar Wakilan Kafafan Yada Labarai Na Jihar Kano,wato Correspondents’ Chapel,a garin Kaduna.
A lokacin taron na kwana biyu, masana sun gabatar da Makaloli dabam-dabam wadanda suka nusar da Wakilan hanyoyin da za su inganta aikinsu na rubutawa da buga labarai.
Daga cikin Makalolin har da wadda Dr.Aminu Ibrahim Shehu,wanda ke aiki a Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke Kano,wato AKTH, ya kawo, wadda ta koya wa Wakilan yadda za su kula da lafiyarsu yayinda su ke gudanar da aikinsu na rubutawa da buga labarai.
Sai kuma Hajiya Sani,wata kwararriyar “Yar Jarida ce, wadda ta nusar da Wakilan game da shigowar Manhajar nan ta AI da kuma yadda za su rika amfani da ita wajen gudanar da aikinsu.
Farfesa Sule Ya’u Sule na Jami’ar Bayero ta Kano,wato,BUK, shi ma ya gabatar da Makala wadda ta koya wa Wakilan yadda za su rika mu’amala da Gwamnatin Jihar Kano cikin sauki ba tare da aikinsu ya tawaya ba.
Daga nan sai wani kwararren Dan Jarida,wato Alhaji Abdullateef Abubakar Jos,da kuma wani kwararren Lauya kuma Dan Jarida, Yusuf Abdulsalam, wadanda su ka koya wa Wakilan dabarun nemo labarai da wallafasu,ba tare da muzguna wa mutane ko bata musu suna ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bude taron,inda ya yabawa Wakilan kan yadda su ke yada sahihan labarai game da Gwamnati da mutanen Jihar Kano.
Gwamnan,wanda Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya wakilta,ya ce Gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafawa Wakilan ta hanyoyin da su ka dace,ta yadda za su ji dadin gudanar da aikinsu.
A cikin jawabinsa na maraba,Shugaban Kungiyar Wakilan Kafafan Yada Labaran na Jihar Kano, Alhaji Murtala Adewale,ya ce an shirya taron ne domin a bai wa “Yan Kungiyar damar samun karin ilimin gudanar da aikinsu, sannan kuma su samu su sarara daga ruguntsumin nemo labarai da wallafasu.
Daga karshe, Alhaji Murtala Adewale ya gode wa Gwamnatin Jihar Kano saboda irin goyon baya da taimakon da ta ke bai wa “ya kungiyar tasa,wanda ya ce ya na agaza musu kwarai wajen samun nasara a cikin aikinsu na Jarida.
