2027:”Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano Na APC Sabbi Da Tsaffi Sun Fara Ziyarce-Ziyarce Don Hadin Kan “Yan Jam’iyya
Daga Abdullahi Yusuf
Kungiyar “Yan Majalisar Dokokin Jihar Kano na APC na da, da na yanzu, ta fara kai ziyarar ban girma ga gaggan Jam’iyyar da ke zaune a birnin tarayya, Abuja,a wani yunkuri na hada kan “Yan Jam’iyyar.
Wannan Labari ya na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Kungiyar,kuma tsohon Kakakin Majalisar,Alhaji AbdulAziz Garba Gafasa,ya rabawa “Yan Jarida a Kano,ranar Juma’ar nan.
Gafasa ya ce,tuni Kungiyar ta kai ziyarar ban girma ga jagoran APC na Jihar Kano,tsohon Gwamnan Jihar Kano,kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar na Kasa,Dakta Abdullahi Umar Ganduje, domin cimma burin da su ka sanya a gama.
Ya kara da cewa Kungiyar kuma ta kai irin wannan ziyara ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai,Barau Jibrin,da kuma
Mataimakin Dan Takarar Gwamnan Jihar Kano a karkashin tutar APC a zaben 2023,wato Murtala Sule Garo.
Shugaban Kungiyar ya ce babban makasudin wadannan Ziyarce-Ziyarce shi ne domin a assasa wani dandamali na hadin kan “Yan Jam’iyyar APC na Jihar Kano, domin tunkarar zaben shekarar 2027.
“Saboda dole ne mu hada kanmu domin mu tunkari zaben shekarar 2027, kuma mu cinyeshi,mu dawo da mulkin APC a Jihar Kano.
“Za mu cinma wannan buri in na mu saboda har yanzu Jam’iyyar APC ce ke da rinjayen magoya baya a Jihar Kano,” in ji tsohon Shugaban Majalisar ta Jihar Kano.
