2027:Dungurawa Ya Ce APC Na Bukatar Kwankwaso Don Ta Ci Zabe
Daga Abdullahi Yusuf
Shugaban Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano,Alhaji Hashimu Suleiman Dungurawa,ya ce Jam’iyyar APC ta na bukatar Shugaban Kwankwasiyya na duniya baki daya,Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin ta ci zaben Shugaban Kasa na shekarar 2027.
Dungurawa ya ce hakan ya kasance ne kuwa, saboda babu wani Dan Siyasa Mai goyon bayan “Yan Nigeria kamar Sanata Rabiu Kwankwaso.
Ya yi wannan ikirari ne kuwa yayin da ya ke ganawa da manema labarai a cikin Ofishinsa ranan Al’hamis din da ta wuce.
“A halin da a ke ciki, Jam’iyyar APC ta rude kuma ta rasa alkibla, saboda haka ta na bukatar wanda zai yi mata jagora domin ta ci Zaben Shugaban Kasa na shekarar 2027,shi ya sanya ta ke neman Jagoranmu,Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, da ya zo ya rike mata tuta.
“Amma Sanata Kwankwaso bai taba neman ya koma APC ba,ita APC din ce da kanta ta ke nemansa da ya dawo cikinta saboda ta gane mahimmancinsa,” in ji Shugaban Jam’iyyar ta NNPP.
Ya ce hakan ta kasance ne saboda APC ta gaza a wajen mulkin Nigeria tun da ta hau karaga mulki fiye da shekaru goma da su ka wuce.
“Tun da APC karbi mulkin Nigeria “Yan Kasa su ke ta fama da talauci,tabarbarewar tattalin arziki da kuma rashin tsaro, kuma ta kasa yin maganinsu,” in ji shi.
Saboda haka, Shugaban Jam’iyyar ta NNPP ya yi kira ga “Yan Nigeria da su yi wo dafifi su karbi Katin Zabe, domin su sami damar zaben Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin Shugaban Kasa a shekarar 2027, domin ya yi maganin wadannan da ma sauran matsalolin da su ke addabarsu.
Daga nan sai Dungurawa ya yi maraba da Kasafin Kudin shekarar 2026 da ke dauke da kimanin N1.368 tiriliyan, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar wa Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Ya ce, Kasafin Kudin ya kunshi kudire-kudire masu mahimmanci wadanda za su inganta rayuwar Jama’ar Jihar Kano,ciki har da samar da ruwan sha, hanyoyi, kiwon lafiya, harkokin noma,ilimi da kuma tallafa wa mata da matasa.
